Jami’an kasar ta Ukraine sun sanar da cewa, da sanyin safiyar Juma’a ne kasar Rasha ta kaddamar da sabbin hare-hare da makamai masu linzami kan kasar Ukraine, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wani yaro dan shekara 10 a birnin Kharkiv dake arewa maso gabashin kasar tare da lalata kayayyakin hatsi da tashar jiragen ruwa a yankin Odesa da ke kudancin kasar.
Wani harin da jirgin mara matuki ya kai ya lalata wani silo na hatsi a gundumar Izmail na yankin Odesa, in ji gwamnan yankin Oleh Kiper.
Hare-haren sun biyo bayan harin makami mai linzami da Rasha ta kai ranar Alhamis inda jami’an Ukraine suka ce an kashe mutane 51 a wani kauye da ke Arewa maso Gabashin Ukraine a yayin wani taron makokin wani sojan Ukraine da ya mutu.
Sanarwar da rundunar sojin sama ta fitar ta ce, a cikin sabbin hare-haren da sojojin saman Ukraine suka kai, sun harbo jiragen sama marasa matuka guda 25 daga cikin 33 da Rasha ta harba daga yankin Crimea da ta mamaye.
A wani harin na daban da aka kai a birnin Kharkiv, an jikkata mutane 16 baya ga yaron mai shekaru 10 da aka kashe, in ji gwamnan yankin Oleh Synehubov.
Ya ce akwai wani jariri dan wata 11 a cikin wadanda suka jikkata kuma an lalata gidaje da motoci.
Moscow ta musanta kai wa fararen hula hari da gangan, amma an kashe da yawa a hare-haren da aka kai a wuraren zama da makamashi, tsaro, tashar jiragen ruwa, hatsi da sauran wurare.
REUTERS/Ladan Nasidi.
Leave a Reply