Gwamnatin jihar Katsina ta jaddada kudurinta na inganta duk wani yanayi na muhalli domin bunkasa tattalin arziki da inganta zaman lafiyar al’ummar jihar.
Kwamishinan ma’aikatar muhalli ta jihar Katsina, Honorabul Musa Adamu Funtua shine ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai a birnin Katsina.
Kamar yadda kwamishinan ya bayyana ingantaccen muhalli shine kashin bayan zaman lafiya da cigaban kowace al’umma.
Yace gwamnatin jihar kalkashin jagorancin gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Radda ta samar da wani kyakkyawan tsari domin tabbatar da muhalli ya inganta a fadin jihar.
“Maganar dashen itatuwa da kwashe shara da magance zaizayar kasa da kuma inganta shi kanshi muhallin rayuwa ce, idan zaizayar kasa ta lalata muhalli ko baka da dajin da zakayi noma ko kuma yanayin ya gurbace to mutane fa sun shiga matsala.
“Mun zagaye fadin jihar Katsina duk mun gano matsalolin kuma zamuyi bakin kokarin mu wajen magance su”, inji Musa Adamu.
Yace a bangaren inganta muhalli gwamnatin jihar kalkashin wani shiri na “ACreSAL” na gudanar da wasu manyan ayyuka a manyan hanyoyin ruwa akan kudi sama da naira biliyan ashirin da shidda (#26,000,000,000) a cikin garin Katsina da Jibia, akwai kuma ayyuka na inganta muhalli na yau da kullum wato “Ecological” a bangaren wasu magudanan ruwa da magance zaizayar kasa, akalla guda 47, a yankunan jihar daban daban wadanda dukkanin su sun taba rayuwar al’ummar jihar.
Kwamishinan muhallin yace ma’aikatar muhallin ta shirya kasafin kudi na shekara mai zuwa dai dai da kudurin tsare tsaren gwamnatin jihar a bangaren inganta muhallin domin zaman lafiya da cigaban jihar
“A bangaren tsabtar muhalli da kauda shara a fadin jihar nan, a yanzu mun gama gano matsalolin kuma muna kan samar da wani shiri mai dorewa domin tabbatar da tsabtar muhalli a fadin jihar nan”, inji shi.
Kamilu Lawal.
Leave a Reply