‘Yan awaren Kamaru dauke da makamai sun ce sun kashe fararen hula biyu da aka yi garkuwa da su a bainar jama’a da suka zarga da yi wa sojoji leken asiri.
Wani ma’aikaci a kauyen Guzang da ke arewa maso yamma ya ce ana gudanar da bincike.
Hakan ya biyo bayan fitar da wani faifan bidiyo da ya nuna wasu mutane biyu zaune a kan titi sannan aka harbe su a kusa da wurin.
Tun a shekarar 2017 ne ‘yan awaren ke fafatawa a yankuna biyu na kasar Kamaru masu magana da Ingilishi.
Sama da mutane 800,000 ne suka rasa matsugunansu.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun yi Allah wadai da sojojin gwamnati da ‘yan aware da kisan gilla, fyade, azabtarwa da kona gidaje da makarantu.
BBC/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply