An gudanar da zanga-zangar kin jinin luwadi a kofar kotun kolin da ke Nairobi babban birnin kasar Kenya.
Kungiyoyin farar hula da na addini da dama na nuna bacin ransu kan wani hukunci na baya-bayan nan wanda ya baiwa kungiyoyin ‘yan luwadi da madigo damar yin rajista a kasar.
Wasu masu zanga-zangar na rike da allunan kira ga alkalan kotun koli da su yi murabus.
Shekaru 10 da suka gabata wata kungiya da ke samun tallafi daga gwamnati ta ki yin rijistar wata kungiyar kare hakkin LGBTQ tana mai cewa tana inganta dabi’ar jinsi daya a kasar da ta haramta luwadi.
Sai dai alkalai a bana sun soke wannan hukuncin.
Shugaban kasar Kenya William Ruto ya bukaci shugabannin addinai su inganta abin da ya kira dabi’u na gargajiya.
BBC/Ladan Nasidi.
Leave a Reply