Dakarun Rasha sun kai wani hari da makami mai linzami na dare a yankin Odesa da ke kudancin Ukraine, lamarin da ya lalata ababen more rayuwa a tashar jiragen ruwa, in ji hukumomin Ukraine.
Gwamna Oleh Kiper ya ce mutane hudu ne suka jikkata sakamakon harin, wanda ya rutsa da wani gidan kwana da wani wurin sayar da hatsi a bakin teku.
A halin da ake ciki kuma rundunar sojin Ukraine ta ce harin ya hada da makami mai linzami na Onyx da aka harba daga yankin Crimea da Rasha ta mamaye.
Sojojin Rasha sun kai hare-hare akai-akai da makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan ababen more rayuwa a tashar jiragen ruwa a cikin ‘yan makonnin da suka gabata, lamarin da ya sa kasar Ukraine ke da wahala wajen fitar da kayayyakinta zuwa kasashen waje.
Rahoton ya ce Mosko ta yi watsi da yarjejeniyar a tsakiyar watan Yuli wadda ta ba da damar jigilar hatsi da kuma taimakawa wajen magance matsalar abinci a duniya.
REUTERS/Ladan Nasidi.
Leave a Reply