Gwamnatin Najeriya ta ce ta shirya gudanar da babban taron noma da samar da abinci na kasa na farko don inganta walwalar manoma, da inganta samar da abinci, da magance wasu kalubalen da ke fuskantar tsarin abinci a Najeriya.
Ministan noma da samar da abinci Abubakar Kyari a Najeriya ne ya bayyana hakan a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya yayin da yake kaddamar da taswirar aikin gona na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
A cewar Kyari, taron kolin noma da samar da abinci na kasa “yana fatan hada dukkan masu ruwa da tsaki domin bunkasa shirin samar da abinci na kasa tare da aiwatarwa da dabarun dorewa.”
Ya ce an shirya taron ne domin neman sha’awa da goyon bayan duk masu ruwa da tsaki a harkar noma a Najeriya, da mai da hankali kan samar da abinci, da abinci mai araha da aminci, da walwalar manoma.
“An shirya taron ne da gaske don neman sha’awa da goyon bayan duk masu ruwa da tsaki a harkar noma da samar da abinci a Najeriya a yunkurinmu na samar da makomar abinci mai gina jiki mai araha da aminci tare da mai da hankali kan jin dadin manoma.”
Taron da aka shirya gudanarwa a watan Nuwambar 2023 shine Shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu GCFR ne ya bude shi kuma ana sa ran zai yi takamammen sanarwa tare da bayyana kiran da ake sa ran daukar mataki ga dukkan masu ruwa da tsaki.
Ministan ya kara da cewa nan da makwanni masu zuwa za a kaddamar da tashar taron kolin don fara ayyukan share fagen taron.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply