Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan harin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a Anguwar Dankali da ke karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.
An bayar da rahoton mutuwar mutane hudu tare da jikkata biyar a harin.
Shugaban majalisar ya ce; “Ya isa” kashe kashen da ake yi a Zariya da sauran sassan kasar nan. Ina kira ga hukumomin tsaro da su “sauka kan masu kisan.”
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan fashin ne suka kai farmaki kan al’ummar yankin, inda suka harbe mutane tara tare da yin awon gaba da wasu biyar, inda daga bisani suka tsere bayan isowar jami’an tsaro da suka yi artabu da maharan da bindiga.
Yayin da yake bayyana harin na baya-bayan da ya yi yawa, Kakakin Majalisar Abbas ya jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su, da kuma jama’a da gwamnatin jihar Kaduna.
A cikin wata sanarwar manema labarai da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Musa Krishi ya fitar, shugaban majalisar ya nuna matukar damuwa, da yawaitar hare-hare da kashe-kashen ‘yan Najeriya da ‘yan bindiga ke yi.
Kakakin majalisar Abbas ya tuna da zafi, yadda aka kashe wasu daga cikin ‘yan majalisarsa a wani hari da aka kai a farkon watan Agusta.
Shugaban Majalisar ya koka da yadda ake samun kashe-kashe ba a Zariya kadai ba, har ma da sauran sassan kasar nan, inda ya jaddada cewa dole ne a kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Ya ce “Jami’an tsaro su bi diddigin wadanda ake zargin, su kama su a gurfanar da su a gaban kotu. Ya kuma tuhume su da hana asarar rayuka da dukiyoyi a fadin kasar nan.”
Leave a Reply