Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Najeriya Za Ta Samar Da Tallafni kaso Hamsin Cikin Dari Ga Manoman Alkama

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

0 205

Gwamnatin Tarayyar Najeriya za ta samar da tallafi kaso hamsin cikin dari ga manoman alkama a fadin kasar.

 

 

A kokarinta na ganin ta bunkasa shirinta na samar da abinci ga al’ummar Najeriya gwamnatin Najeriya ta kudiri aniyar samar da tallafio kaso hamshin cikin dari ga manoman alkama a fadin kasar.

 

Ministan albarkatun noma da wadata kasa da abinci Abubakar Kyari ya bayyana haka a yayin ziyarar aiki da ya kawo anan Kano Arewa maso Yammacin Najeriya. Yace cikin shekaru hudu zuwa biyar cikin shiri da gwamnatin tarayya ta tsara kasar za ta kawo karshen shigo da iri ta dogara da kanta ta yadda za a wadata kasa da abinci.

 

Da yake jawabi a wannan Juma’a yayin ziyarar da ya kawo jihar ta Kano a ranar Juma’a ministan albarkatun gona da wadata kasa da abinci yace ajandar  Gwamnatin Shugaba Tinubu na da burin ganin Najeriya ta tsaya da kafarta don tabbatar da ganin al’umma sun wadatu da abinci, faraway tun daga watan Nuwamba da za a fara noman rani.

 

Yace gwamnatin taraya na yin yunkuri na samar da irin shukar alkama ga gonaki masu fadin Hekta 70,000 da aka ware don noman alkama. Yace suna aiki tukuru don tabbatar da ganin an samar da irin shuka alkamar anan gida Najeriya.

 

 

Yace gwamnatin taraya na shirin tabbatar da ganin an samar da abinci ga ‘yankasa su dogara da abin da ake samarwa a cikin kasar. A kawo karshen shigo da irin daga kasashen ketare.

 

 

Minista Kyari ya nuna gamsuwa da yadda ake aikin samar da irin shukar ga kasa wanda ya bayyana da zama ginshiki na wannan noma.

 

 

A cewarsa gwamnatin jihar Jigawa Arewa maso Yammacin Najeriya ta taka muhimmiyar rawa

 

 

A noman na alkama ta yadda ta samar hekta 40,000  daga cikin 70,000 da gwamnatin tarayya ta ware don cimma wannan buri a wannan shekara.

 

 

Yayin ziyarar a jihar ta Kano ministan Kyari ya kuma ziyarci wasu rumbunan ajiyar irin shukar da suka hada da kamfanin AA Albasu Grain da na Alyumna.

 

 

Yusuf Bala Nayaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *