Take a fresh look at your lifestyle.

Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu Sun Kammala Tattaunawa Kan Yarjejeniyar Cinikayya tsakanin Su

0 115

Hadaddiyar Daular Larabawa da Koriya ta Kudu sun kammala tattaunawa kan yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, wacce aka fi sani da Yarjejeniyar Haɗin gwiwar Tattalin Arziki (CEPA) a cewar ƙasashen biyu.

 

 

Alakar kasuwanci da saka hannun jari tsakanin kasashen yankin Gulf da Koriya ta Kudu na samun ci gaba; Sanarwar ta ce, a farkon rabin shekarar 2023, cinikin da ba na mai ba ya kai dalar Amurka biliyan 3, kwatankwacin lokacin shekarar da ta gabata, amma ya karu da kashi 21% bisa na shekarar 2021.

 

 

A halin da ake ciki, Kamfanin Lantarki na Koriya da kuma hadin gwiwar kamfanonin Koriya sun kuma gina dukkanin rukunin hudu na Kamfanin samar da wutar lantarki na Barakah na dala biliyan 20 a Abu Dhabi, wanda ya fara aiki a watan Afrilu na wannan shekara, don taimakawa wajen tallafawa bukatun wutar lantarki na cikin gida na UAE.

 

 

Koriya ta Kudu ta kasance daya daga cikin kasashen farko da yankin Gulf suka kaddamar da tattaunawa da CEPA a shekarar 2021.

 

 

Sai dai bayan watanni uku, kasar ta Asiya ta sake farfado da yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci (FTA) da kungiyar hadin kan kasashen yankin Gulf mai mambobi shida, wadda hadaddiyar daular Larabawa mamba ce.

 

 

Rahoton ya ce kawo yanzu UAE ta rattaba hannu kan wasu tsare-tsare na CEPA da suka hada da na abokan gaba na siyasa a baya Isra’ila da Turkiyya, zuwa kasashen Asiya Indiya da Indonesiya, a wani bangare na dabarun karkatar da tattalin arzikinta daga man fetur.

 

 

Ta ce ba ta cakude siyasa da kasuwanci lokacin da aka tambaye ta ko rikicin Isra’ila da Gaza zai yi tasiri kan yarjejeniyar kasuwanci da kasashen yankin Gulf da Isra’ila.

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *