Take a fresh look at your lifestyle.

Kungiyar Ci Gaban Iri Domin Kafa Karin ofisoshi

0 176

Kungiyar ‘yan kasuwa da ci gaban iri ta Najeriya SEEDAN, ta ce za ta kafa ofishi mai dauke da kayayyakin aiki a Abuja da kuma na kowane shiyyar siyasa a fadin kasar.

 

Shugaban kungiyar na kasa Alhaji Yusuf Ado Kibiya ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Talata.

 

Baya ga haka, ya bayyana cewa kungiyar ta fara kamfen na wayar da kan manoma da sauran masu ruwa da tsaki kan muhimmancin iri wajen bunkasa noma.

 

Kibiya ya ce wannan gangamin zai fadakar da gwamnati a dukkan matakai kan muhimmancin iri da kuma sanar da manoma sabbin iri.

 

Ya kuma ce kungiyar za ta yi aiki da hukumomin kasa da kasa da abin ya shafa da ke da niyyar taimakawa bangaren iri na kasar.

 

Ya ce “Kungiyar za ta yi aiki tare da cibiyoyin bincike da jami’o’i don bunkasa iri na farko.”

 

A cewarsa, kungiyar za ta yi kokarin daga darajar masana’antar iri ta hanyar hada hannu da cibiyoyin hada-hadar kudi domin samun saukin kudaden shiga.

 

 

 

NAN/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *