Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan jihar Neja Ya Taya Sabon Shugaban VON, Ndace Murna

0 179

Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya mika sakon taya murna ga Jibrin Baba Ndace bisa nadin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi masa a matsayin Darakta-Janar kuma babban darakta na gidan rediyon Muryar Najeriya (VON).

 

 

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran shi, Bologi Ibrahim ya fitar, gwamna Umaru Bago ya bayyana nadin a matsayin wanda ya cancanta. Ya kuma jaddada cewa Baba Ndace kwararre ne dan jarida wanda ya bar tarihi a harkar yada labarai.

 

 

Gwamnan ya bayyana kwarin gwuiwar sa ga cancantar Ndace da kuma damar daukaka VON zuwa wani matsayi.

 

 

Gwamna Bago ya bayyana fatan shi cewa sabon Darakta Janar na VON zai kawo abin alfahari a jihar Neja da Najeriya baki daya. Ya kuma yi alkawarin bayar da dukkan goyon bayan da suka dace don tabbatar da nasarar Ndace a sabon aikin shi.

 

 

Ladan Nasidi.

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *