Take a fresh look at your lifestyle.

Koriya Ta Arewa: Kim Ya Yi Alkawarin Cika Yarjejeniyoyin Da Aka Kulla Da Rasha

0 245

Kafar yada labaran kasar KCNA ta rawaito cewa, shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya bayyana kudurin shia na cika yarjejeniyoyin da aka cimma a taron da ya yi a watan jiya da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a lokacin da ya gana da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da ke ziyara a kasar.

 

 

Kim ya kai wata ziyarar da ba kasafai ba a watan da ya gabata a Rasha inda ya gayyaci Putin zuwa Pyongyang tare da tattauna hadin gwiwar soji, ciki har da shirin tauraron dan adam na Koriya ta Arewa, da yakin Ukraine.

 

 

KCNA ta ce Kim da Lavrov sun tattauna hanyoyin inganta hadin gwiwa don mayar da martani ga al’amuran shiyya-shiyya da na duniya bisa “dangantaka ta siyasa da aminci,” kuma Lavrov ya mika gaisuwar Putin ga Kim, in ji KCNA.

 

Kim ya yi alkawarin samar da tsayayyen tsari, mai hangen nesa, mai nisa ga dangantakar DPRK da Rasha a cikin sabon zamani ta hanyar aiwatar da yarjejeniyoyin da aminci a kuma ci gaba da manufar gina kasa mai karfi,” in ji KCNA.

 

 

Yana magana ne ga Koriya ta Arewa da farkon sunanta, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Koriya.

 

 

KCNA ta ce, ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa Choe Son Hui da Lavrov sun rattaba hannu kan shirin musaya tsakanin shekarar 2024-25, yayin da suke tattaunawa daban-daban don bin diddigin taron da kuma neman karin hadin gwiwa kan tattalin arziki da al’adu da ci gaban kimiyya da fasaha.

 

 

Jami’an diflomasiyyar biyu sun kuma tattauna kan yadda za a dora alakar kasashen biyu “a mataki mafi girma,” in ji shi.

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *