Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Wakilai Ta Bukaci Haramta Amfani Da Litattafan Dake Bata Tarbiyya

Abdulkarim Rabiu, Abuja.

148

Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomin kasar da su sanya dokar hana samarwa a cikin gida, da shigowa ko amfani da duk wani abu na kayan koyo da koyarwa na ilimi da ke inganta ayyukan masha’a irin su Madigo, Luwadi, da Auren jinci a makarantu a fadin Najeriya.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Gumi/Bukkuyum na jihar Zamfara, Hon. Sulaiman Abubakar Gumi, ya gabatar a zauren majalisar ranar Alhamis.

Da yake gabatar da kudirin, Honarabul Gumi ya nuna damuwarsa kan yadda ake shigowa da kayayyakin ilimi daga kasashen waje da ake amfani  da su a makarantun Nursery da Primary a Najeriya wadanda suka saba tsarin koyarwa da inganta wasu dabi’u wadanda suka sabawa ka’idoji da dabi’un Najeriya.

Ya kuma nuna damuwarsa cewa littafin da aka fi amfani da shi, ‘Queen Primer’ a hankali yana gabatar da kalmomi kamar ‘gay’, wato dan Luwadi da  ‘eros’, da sauransu da ke yada dabi’ar lalata da halayen masha’a.

A don haka ‘yan majalisar sun ce wadannan kalmomi suna koyar da yaran da ba su ji ba ba su gani ba, kan dabiun da ba su dace a shekarun su, wanda ya sabawa doka, da rashin da’a da kuma tarbiyyar yara.

 “Akwai bukatar sanyawa da kare kyawawan dabi’u a cikin yara da al’umma gaba daya ta hanyar bijirewa amfani da kayan ilimi da ke koyarwa ko inganta duk wani nau’in dabi’a na bariki wanda ya saba wa dokoki da kyawawan dabi’u a duk cibiyoyin ilimi, musamman a makarantun Nazire da  firamare,” in ji Hon Gumi.

Comments are closed.