Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Dattijai Zata Haɓaka Amfani Da TETFund Yadda Ya Kamata

0 204

Kwamitin majalisar dattijai mai kula da manyan makarantu da asusun tallafawa manyan makarantu (TETFund), ya ce zai gudanar da sahihin sa  ido kan asusun da nufin ganin an yi amfani da shi yadda ya kamata.

 

Shugaban kwamitin Sanata Muntari Dandutse (APC-Katsina) ne ya bayyana haka yayin taron farko na kwamitin da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.

 

Dandutse ya ce, kwamitin zai kuma tabbatar da cewa Asusun ya gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, a bayyane da kuma yadda ya kamata domin kara habaka tasirinsa.

 

“Wadannan cibiyoyi suna buƙatar tallafinmu ba tare da gajiyawa ba domin bunƙasa da daidaita buƙatun al’ummar mu.

 

Hukumar ta TETFund, tare da aikinta na samar da kudaden shiga ga wadannan cibiyoyi, tana taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da ilimi gaba, bincike da ci gaban ababen more rayuwa.

 

“Za mu nemi albarkatu domin inganta ababen more rayuwa da suka lalace a manyan makarantu. Akwai masu ba da taimako da yawa da hukumomi ban da TETFund. Saboda haka za mu tabbatar da cewa an yi amfani da asusun da ke TETFUND,” inji shi

 

Dan majalisar ya ci gaba da cewa, a cikin kwanaki da watanni masu zuwa, kwamitin zai zurfafa bincike kan batutuwa masu sarkakiya da ke fuskantar manyan makarantu da kuma TETFund.

 

A cewarsa; Za mu saurari masana, masu ruwa da tsaki da kuma muryoyin mutanen da muke yi wa hidima.

 

“Za mu yi aiki tukuru don tsara dokoki, ba da shawarwari da kuma sa ido kan yadda ake rarraba albarkatu domin magance waɗannan kalubale.”

 

Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, Simon Mwadkwon (PDP-Plateau) ya ce sanannen abu ne cewa ana tada husuma a manyan makarantu.

 

Sai dai Mwadkwon ya ce kwamitin zai tabbatar da cewa an yi wani abu don ciyar da harkar ilimi gaba.

 

Hakazalika, Sanata Neda Imasuen (LP-Edo) ya bayyana cewa harkar ilimi ta tabarbare, saboda haka ya yi kira da a yi kokarin shawo kan matsalar lalacewa.

 

Ya ce yayin da ake ci gaba da yin mu’amala da jami’o’i, ya kamata a mai da hankali kan matsalar shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa a cibiyoyi daban-daban.

 

 

NAN/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *