Take a fresh look at your lifestyle.

Najeriya Ta Kaddamar Da Ayyukan Noma Na Matasa

0 215

Kungiyar tuntuba kan binciken noma na kasa da kasa, CGIAR, tare da hadin gwiwar Cibiyar Noma ta Kasa da Kasa, IITA, Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya, FAO, Ma’aikatar Aikin Gona da Abinci ta Tarayya da sauran abokan hulda suna kaddamar da ayyukan noma na matasa. YAS, aikin, “wanda aka yi niyya domin ƙarfafawa da tallafawa matasan Najeriya a cikin harkokin Noma.”

 

An yi wannan aikin ne don sanya noma ya zama abin sha’awa ga matasa tare da nuna musu yadda za su mayar da aikin noma kasuwanci mai dorewa.

 

A halin yanzu ana ci gaba da kaddamar da taron a cibiyar IITA da ke Abuja babban birnin Najeriya.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *