Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Gargadin Rufe Asibitocin Gaza Saboda Karancin Man Fetur

0 329

Majalisar Dinkin Duniya, babbar mai ba da agaji a Gaza ta ce aikinta zai tsaya a daren yau idan ba ta samu sabbin kayayyaki ba saboda asibitoci suna dakatar da komai sai ayyukan gaggawa saboda karancin mai.

 

Isra’ila na dakatar da sabbin kayan man fetur zuwa Gaza, amma tana zargin Hamas da tara dubban daruruwan lita.

 

Wasu motocin daukar kaya guda takwas dauke da abinci, ruwa, da magunguna sun tsallaka daga Masar zuwa Gaza a daren jiya amma hukumomin sun ce ana bukatar akalla motocin daukar kaya 100 a rana.

 

Gwamnatin Gaza ta ce mutane 80 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai cikin dare.

 

A ranar Talata, ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce kusan mutane 5,800 ne aka kashe tun ranar 7 ga Oktoba.

 

 

BBC/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *