Take a fresh look at your lifestyle.

Daliban Manyan Makarantu Sun Samu Kyaututtuka Da Tallafin Karatu Na Musamman A Jihar Katsina

Kamilu Lawal,Katsina.

151

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya kaddamar da wani sabon shirin bada tallafin naira dubu hamsin hamsin ga dalibai da suka nuna hazaka daga cikin daliban manyan makarantun jihar

 

Daliban wadanda suka amfana sune wadanda suka samu sakamako ajin farko mai maki 4.50 zuwa sama a zangon karatun su

 

Da yake mika kyautar kudaden da lambobin yabon ga wadanda suka amfana da tallafin na musamman a ofishin hukumar bada tallafin karatu a makaratun gaba da sakandire ta jihar Katsina, Babban darektan hukumar, dakta Aminu Tsauri ya bayyana cewa gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ne ya bada kudin ga dalibai 210 da suka yi fice a karatunsu ta hanyar samun sakamakon mai maki 4.50 CGPA zuwa sama  a manyan makarantun dake jihar.

 

 

Yace bayar da kyaututukan da kudaden tallafin na musamman na da nufin zaburar da daliban su kara azama wajen maida hankali ga karatunsu ta hanyar yin gogayya domin ganin sun samu kyaututtukan da kuma tallafin karatun na musamman da gwamnan jihar ya samar.

 

“Wannan kyauta da mai girma gwamna ya bayar ga hazikan daliban na da manufar sanya azama a tsakanin su domin a kara samun hazikai masu gogayya wajen karatun su”, inji Dr. Tsauri.

 

Bayar da kyaututtukan wanda aka gudanar yan sa’o’i bayan da gwamnan jihar malam Dikko Radda ya kaddamar da shirin hadi da rabon tallafin karatu na shekara shekara ga daliban jihar.

 

 

Babban darektan yace a wannan karon gwamnan ya amince da biyan daliban har na shekaru biyu a manyan makarantun, yana mai cewa sama da naira miliyan dari shidda da arba’in ne gwamnan jihar ya amince domin biyan daliban.

 

“Mu na da kashi ukku na tallafi domin daliban, na farko shine wanda mai girma gwamna ya kaddamar domin baiwa dukkanin daliban manyan makarantun wanda shine wannan hukuma tamu zata basu, sai kuma na bangaren kyaututtuka daga mai girma gwamna da wasu yan majalisa da sauran masu ruwa da tsaki a jihar nan zasu baiwa daliban”, inji shi.

 

Dakta Aminu Tsauri ya bukaci daliban da suka amfana da suyi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace domin tallafawa shirin gwamnatin jihar na tabbatar matasan jihar sun samu guraben manyan makarantu har zuwa kammalawa.

 

 

Kamilu Lawal.

Comments are closed.