Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Rt. Hon. Balarabe Abdullahi, ya yaba da hukuncin kotun koli da ta tabbatar da shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya.
Rt. Hon. Abdullahi yayin da yake mayar da martani kan hukuncin kotun koli, ya taya shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettimah murnar nasarar da suka samu.
KU KARANTA: Zaben shugaban kasa: Ra’ayoyin da suka biyo bayan hukuncin kotun kolin Najeriya.
Ya kuma jinjina wa jam’iyyar APC mai mulki da ‘yan Najeriya, inda ya bayyana hukuncin kotun a matsayin tabbaci da kuma bayyana wa’adin da al’ummar kasar nan suka baiwa shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kakakin majalisar ya yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su marawa shugaba Tinubu baya domin a yanzu ya zauna ya yi cikakken harkokin mulki ba tare da wata tangarda ba.
Ya kuma yabawa lauyoyin jam’iyyar APC bisa namijin kokarin da suka yi da kuma bangaren shari’a kan wannan hukunci mai matukar muhimmanci, wanda a cewarsa, ya nuna buri da muradin ‘yan Najeriya da dama.
Ladan Nasidi.
Hello! Are you looking for a business trip massage in Gyeonggi Province? We are dedicated to serving our customers 24/7, 365 days a year. We offer a variety of massage services and events, prioritizing customer satisfaction above all.