Dan majalisa Ya Sha Alwashin Inganta Rayuwar Al,ummar Mazabar Katsina Ta Tsakiya
Kamilu Lawal,Katsina.
Wakilin mazabar Katsina ta tsakiya a majalisar wakillai ta Abuja wanda wata kotun daukaka kararrakin zabe ta tabbatarwa da nasara a ranar alhamis data gabata, Honorabul Sani Aliyu Danlami, ya bayyana cewa idan aka rantsar dashi zai gudanar da wakilci dai dai da bukatun al’ummar mazabar sa
Ya bayyana shirin sa na shiga cikin al’umma domin jin matsalolin su da nufin warware masu su.
” Al’ummar Katsina zata ga wakilci daga gare ni wanda kuma za suyi alfahari da shi, zamu tabbatar da ingantuwar rayuwar al’umar wannan mazaba kamar samawa matasa aikin yi da inganta harkar lafiya da bangaren ilmi da samar da ruwan sha”, inji Danlami.
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya samu tarba daga dandazon magoya bayan sa a filin jirgin sama na tunawa da malam Umaru Musa Yar’adua dake Katsina bayan da wata kotun daukaka kara dake Abuja ta bayyana shi a matsayin halastaccen wakilin mazabar Katsina ta tsakiya.
Sani Danlami yayi alkawalin gudanar da wakilcin bisa adalci ba tare nuna banbanci a tsakanin magoya bayan jam’iyyu ba a mazabar ta Katsina.
Kamar yadda Hon.Danlami ya bayyana; “da dan APC da yan sauran jam’iyyu, da wanda ya zabe ni da wanda bai zabe ni ba, a yanzu duk sun zama daya a gareni, amanar su na hannu na kuma ina tabbatar masu da cewa zan yi masu wakilci na adalci a majalisar wakillan najeriya da izinin Allah”.
Dan majalisar ya bukaci hadin kan al’umma ta hanyar bashi shawarwari masu ma’ana domin cigaban al’ummar mazabar da jihar Katsina baki daya
Idan dai za’a iya tunawa a makon da ya gabata ne kotun daukaka kararrakin zabe ta tabbatar da hukuncin kotun zabe ta “tribunal” wanda ta bayyana Hon. Sani Danlami a matsayin halastaccen zababben dan majalisar mazabar
Hakan ya biyo bayan shigar da korafi da yai yana kalubantar sakamakon takardar makarantar firamare ta abokin takararsa na PDP Hon. Aminu Cindo wanda hukumar zabe ta bayyana a matsayin zababbe a zaben watan fabrairu da ya gabata.
Aminu Cindo dai ya gaza tabbatarwa kotunan biyu ingancin takardar karatun tasa, dalilin da yasa kotun daukaka karar ta umarci hukumar zaben ta baiwa Sani Danlami takardar samun nasara domin a rantsar dashi a matsayin wakilin mazabar Katsina central a majalisar wakillan ta najeriya.
Kamilu Lawal.
Leave a Reply