An kama madugun ‘yan adawar Bangladesh da wasu ‘yan jam’iyyar shi da dama bayan zanga-zangar adawa da gwamnati a Dhaka.
Mirza Fakhrul Islam Alamgir, Sakatare Janar na Jam’iyyar Bangaladesh Nationalist Party (BNP), yana cikin wadanda ke fuskantar tuhuma, in ji wani jami’in.
Dubun dubatar masu zanga-zanga ne suka fito a karshen mako, suna kira ga firaminista Sheikh Hasina ta yi murabus.
An kashe dan sanda daya, da kuma a kalla daya daga cikin masu zanga-zangar.
Akwai rahotanni masu karo da juna kan dalilin da ya sa aka kama Mista Alamgir mai shekaru 75.
Kafofin yada labaran cikin gida sun ba da rahoton cewa an tsare shi ne bisa zargin kai hari a gidan alkalin alkalan Bangladesh.
Sai dai kamfanin dillancin labaran AFP ya ce an tuhume shi tare da wasu mambobin jam’iyyar BNP su 164 da laifin kisan kai bayan mutuwar dan sandan a zanga-zangar ta ranar Asabar.
‘Yan sanda sun ce an kashe dan sanda har lahira, kuma sun zargi masu fafutukar BNP da kisan.
Masu zanga-zangar da ‘yan sanda sun sake yin artabu a ranar Lahadi a wurare da dama. Mutane da dama sun jikkata.
Ms Hasina ‘yar Shugaban Bangladesh ta farko ta kasance a kan karagar mulki tun shekara ta 2009, kuma ana zargin ta da kai hari kan masu fafutuka da ‘yan adawar siyasa, abin da ta musanta.
Siyasar Bangladesh ta dade tana fama da rashin jituwa tsakanin Ms Hasina da Ms Zia, wadanda dukkansu suka yi aiki a matsayin Firayim Minista.
BBC/Ladan Nasidi.
Leave a Reply