Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce ana ci gaba da kai hare-hare ta sama da Isra’ila a yankin da ke kusa da wani muhimmin asibiti a birnin Gaza yayin da ma’aikatan suka yi gargadin cewa kwashe marasa lafiya daga wurin ba zai yiwu ba.
Isra’ila ta gaya wa ma’aikata da su kwashe majinyata daga asibitin Al-Quds a ranar Lahadin da ta gabata amma likitoci sun ce korar daruruwan marasa lafiya wadanda yawancin su ke cikin kulawa ba zai yiwu ba.
Kimanin fararen hula 14,000 kuma an fahimci cewa suna matsuguni a asibitin da harabar shi.
Isra’ila dai na kai hare-hare a Gaza tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
Ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce sama da mutane 8,000 ne aka kashe tun lokacin da Isra’ila ta fara kai harin ramuwar gayya.
BBC/Ladan Nasidi.
Leave a Reply