Take a fresh look at your lifestyle.

Afirka Ta Kudu Ta Yi Kira Ga Majalisar Dinkin Duniya Da Ta Kare Gaza

0 168

Afirka ta Kudu ta ce ya kamata Majalisar Dinkin Duniya ta tura abin da ta kira “Rundunar kariya cikin gaggawa” domin shiga tsakani a rikicin Isra’ila da Gaza “domin kare fararen hula daga ci gaba da kai hare-hare”.

 

A cikin wata sanarwa mai zafi, ma’aikatar hulda da kasashen duniya ta bayyana adadin yaran da aka kashe ya zuwa yanzu a rikicin tare da zargin Isra’ila da keta dokokin kasa da kasa.

 

Isra’ila ta kare harin bama-bamai da kuma mamayar kasa da ta kai Gaza bisa hujjar kariyar kai, bayan kashe mutane 1,400 da Hamas ta yi a ranar 7 ga Oktoba. An yi garkuwa da mutane 230 .

 

Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce sama da mutane 8,000 ne aka kashe tun bayan fara harin ramuwar gayya na Isra’ila.

 

 

BBC/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *