Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar Da Kayode Egbetokun A Matsayin Babban IGP

68 499

Majalisar Kula Da ‘Yan Sanda Ta Kasa ta tabbatar da tsohon mukaddashin Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun a matsayin Babban IGP Kuma Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.

Da yake karin haske ga manema labarai na fadar gwamnatin jihar bayan kammala taron majalisar, ministan harkokin ‘yan sanda, Ibrahim Geidam ya sanar da tabbatar da Kayode Egbetokun a matsayin Babban Sufeto Janar Na ‘Yan Sanda.

Geidam ya kuma ce “Mambobin sun amince da kudirin Shugaba Tinubu kan tabbatar da Mista Egbetokun bayan bin ka’idarsa da gogewar aikinsa.”

Ya ce tabbatar da Egbetokun ya biyo bayan gamsuwar da ya yi a bakin aiki a cikin watanni uku da suka gabata tun bayan nadin da aka yi masa a ranar 20 ga watan Yuni.

Geidam ya ci gaba da cewa, IGP din wanda ya shafe watanni 3 zuwa 4 yana aiki a matsayin mukaddashin tun bayan nadin nasa, ya gabatar da bayanai masu ban sha’awa da suka bayyana dimbin shirye-shiryensa na ayyukan ‘yan sanda da na tsaro, wanda hakan ya sanya shi ya kware sosai.

A ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, 2023, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Egbetokun a matsayin IGP.

Sabon IGP ya maye gurbin Usman Baba, wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a ranar 6 ga Afrilu, 2021.

An haife shi a ranar 4 ga Satumba, 1964 daga karamar hukumar Egbado ta kudu a jihar Ogun, a kudu maso yammacin Najeriya, Egbetokun ya shiga aikin ‘yan sandan Najeriya a matsayin Cadet ASP (Course 16) a ranar 3 ga Maris, 1990.

Zai cika shekaru 35 yana aiki a watan Satumba 2024, bisa ga dokokin ‘yan sanda.

 

68 responses to “Hukumar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar Da Kayode Egbetokun A Matsayin Babban IGP”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *