Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Dinkin Duniya Ta Damu Matuka Da Isra’ila Ta Mayar Da Ma’aikata Falasdinawa Zuwa Gaza

0 85

Ofishin kare hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ma’aikatan Falasdinawa da Isra’ila ta mayar da su Gaza ba za su samu gidajen da za su koma ba da kuma fuskantar hadari mai tsanani daga ci gaba da fada a yankin.

 

“Na fahimci cewa a cikin wadannan mutanen da ake mayar da su akwai ma’aikatan Falasdinawa da majinyata asibitoci da aka tsare bayan ranar 7 ga Oktoba,” in ji kakakinta Elizabeth Throssell ga manema labarai a Geneva.

 

“Mun damu matuka cewa a kalla ma’aikatan Falasdinawan 4,000 da majinyata asibiti ana tsare da su ba tare da isassun ka’idojin doka ba a wuraren soji bayan da Isra’ila ta kwace musu izini,” in ji ta.

 

Throssell ya kara da cewa “Akwai rahotanni masu tayar da hankali cewa ana mayar da wasu zuwa Gaza, duk da tsananin yanayin da ake ciki.”

 

“Ba mu san takamaimai zuwa ina ba; mai yiwuwa ba a bayyana ko sun sami ko da gidan da za su je ba; kuma lamari ne mai matukar wahala da hadari.”

 

 

 

ALJAZEERA/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *