Take a fresh look at your lifestyle.

Isra’ila Ta kashe Falasdinawa 10 A Yammacin Gabar Kogin Jordan Da Ta Mamaye

0 128

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kashe Falasdinawa akalla 10 tare da jikkata wasu da dama a yankin yammacin gabar kogin Jordan da suka mamaye a wani samame da kuma arangama da suka yi cikin dare a ranar Juma’a.

 

Akalla mutane biyar ne aka kashe a Jenin inda sojojin Isra’ila suka tarwatsa gidajen Falasdinawa biyu da ake nema ruwa a jallo tare da rusa akalla guda uku a ciki da kuma kusa da sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin, kamar yadda wasu majiyoyi na cikin gida suka shaida wa Al Jazeera a ranar Juma’a.

 

Majiyoyin sun ce farmakin wanda shi ne na shida cikin makonni biyu da suka gabata a Jenin, an fara shi ne da misalin karfe 22:00 agogon GMT, kuma ya dauki tsawon sa’o’i tara.

 

An dade ana kallon sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin a matsayin wani tungar gwagwarmayar Falasdinawa, fiye da shekaru biyun da suka wuce lokacin da mayaka suka fara aiki ba tare da bata lokaci ba domin tunkarar sojojin mamaya na Isra’ila.

 

A sansanin ‘yan gudun hijira na al-Fawwar da ke kudancin Hebron, Sojojin Isra’ila sun yi arangama da Falasdinawa kusan sa’o’i uku, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu akalla biyar, kamar yadda majiyoyin lafiya suka shaida wa Al Jazeera.

 

Sojojin Isra’ila sun tsare akalla Falasdinawa uku da suka hada da iyayen wani Bafalasdine da ake nema ruwa a jallo, dabarar da suka shafe shekaru suna amfani da ita, domin matsawa Falasdinawa da su mika kansu a cewar majiyoyin cikin gida.

 

A sansanin ‘yan gudun hijira na Qalandiya da ke arewacin Gabashin Kudus da aka mamaye, an kashe Bafalasdine guda tare da jikkata wasu da dama a wani samame da aka kai da sanyin safiyar yau.

 

Wani Bafalasdine kuma ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a ranar Laraba yayin wani samame da Isra’ila ta kai kan Nablus.

 

A kauyen Budrus da ke arewa maso yammacin Ramallah, majiyoyin kiwon lafiya sun shaidawa Al Jazeera cewa Sojojin Isra’ila sun kashe wani Bafalasdine, yayin da wasu biyu suka jikkata.

 

Mazauna yankin sun ce Falasdinawa na shirin yin sallar Juma’a ne a daidai lokacin da sojojin Isra’ila ke kai farmaki a kauyen, sai aka ji harbe-harbe guda uku.

 

Sojojin Isra’ila sun kai farmaki a Tulkarm kuma ana ci gaba da arangama.

 

Isra’ila ta mamaye Yammacin Kogin Jordan tun bayan yakin Larabawa da Isra’ila a shekara ta 1967 kuma Dakarunta na kai hare-hare a cikin al’ummar Falasdinawa a can.

 

 

Tun a farkon shekarar da ta gabata tashe-tashen hankula a Yammacin Kogin Jordan ke karuwa, inda ake yawan kai hare-hare da sojoji, da hare-haren ‘yan Isra’ila da Falasdinawan suka kai kan Sojoji da matsugunan Isra’ila.

 

Sama da Falasdinawa 140 ne aka kashe a yammacin gabar kogin Jordan tun bayan fara yakin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba.

 

Tun daga wannan lokacin, ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce fiye da mutane 9,000 ne aka kashe a harin bam da Isra’ila ta kai, kashi biyu bisa uku na mata da yara.

 

 

 

ALJAZEERA/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *