Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom da ke kudu maso kudu, Najeriya ya bayyana shirin gwamnatin sa na yin hadin gwiwa da bankin duniya domin bunkasa noma da tabbatar da samar da abinci a jihar.
Eno ya sanar da cewa ya amince da kudi naira miliyan 450 a matsayin takwaransa na asusun ‘Nigeria for Women Project’ wanda bankin duniya ke taimakawa.
A cewar wata sanarwa da sashin yada labarai na gidan gwamnati ya fitar a karshen mako a garin Uyo, gwamnan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar bankin duniya karkashin jagorancin daraktan kula da harkokin Najeriya, Shudham Chaudhury, a fadar gwamnati dake Uyo.
Kalamansa: “Yawancin shirye-shiryen irin ku da kuka lura suna yaba Ajandar mu ta A.R.I.S.E. Mun shirya mu yi aiki tare da ku don tabbatar da cewa mun ci gaba da haɓaka a inda ya cancanta.
“A yanzu, noma shine babban abin da A.R.I.S.E ajandar ke magana akai. Za mu iya yin aiki tare da Bankin Duniya don haɓaka ayyukan noma da tabbatar da wadatar abinci a cikin Jiha.
“Hakika wannan ziyarar ta ba da haske sosai kan ayyukan Bankin Duniya a Akwa Ibom kuma dole ne in ce a cikin watanni biyar da na yi a ofis, wannan ne karo na farko da nake samun irin wannan bayanin kan ayyukan Bankin Duniya da muke yi.
“Sauraron ku a cikin wannan taron ya ba mu, musamman ni kaina, damar samun fahimtar yadda waɗannan abubuwan ke gudana. Muna iya tabbatar muku da cewa za mu toshe guraben da aka samu, kuma a lokacin da za ku yi tantancewar ku na gaba, za ku gan mu cikin sauri.
“Akan naira miliyan 450 da ya kamata a ba da gudummawar, na san na ba da izini kuma zan iya gaya muku nan da mako guda mai zuwa za mu bayar da shi.
“Ina mai tabbatar muku da cewa za mu yi aiki tukuru, kuma zan nada babban mataimaki na musamman wanda zai yi aiki a matsayin mai kula da harkokin jiha don taimakawa wajen daidaita wadannan ayyuka tare da kawo min rahoto kai tsaye kan dukkan wadannan ayyuka domin mu ga gibin da ke akwai. kuma ku fahimci yadda ake saurin rufe su”.
Da yake jawabi tun da farko, Daraktan Bankin Duniya, Mista Shudham Chaudhury, ya bayyana cewa ziyarar na da nufin raba iliminsa da gwamnatin Gov Eno tare da yin bayyani kan tallafin da bankin ke baiwa Najeriya wajen ciyar da kasa da kasa gaba.
Vanguard/Ladan Nasidi.
Leave a Reply