Take a fresh look at your lifestyle.

GWAMNA MAKINDE YA KARBI BAKUNCIN ATIKU, OKOWA, DA MEMBOBI PDP NA NWC

0 90

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a safiyar Laraba, ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a gidan gwamnati dake Agodi, Ibadan, babban birnin jihar.

Atiku ya isa gidan gwamnatin Oyo ne tare da abokin takararsa, Ifeanyi Okowa da misalin karfe 11:46 na safe.

Tun da farko mataimakin gwamnan jihar, Bayo Lawal, tare da wasu manyan jami’an gwamnati ne suka tarbi masu ziyarar a filin jirgin sama na Ibadan, Alakia, a madadin gwamnan.

Bayan isa gidan gwamnati, Gwamna Makinde ya jagoranci manyan ‘yan tawagar da suka kai ziyarar, ciki har da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, zuwa wani daki mai zaman kansa, inda aka yi wata ‘yar gajeruwar ganawa, wanda ya dauki tsawon mintuna 15 ana yi.

Bayan fitowa daga dakin da ke ciki, Gwamnan ya bayyana cewa dukkan tawagar za su tashi zuwa dakin taro na Theophilus Ogunlesi, daura da Asibitin Kwalejin Jami’ar Ibadan, inda aka bukaci Atiku ya yi jawabi ga wakilan Kudu maso Yamma.

Wasu daga cikin jiga-jigan a fadar gwamnatin Oyo sun hada da, Gwamna Aminu Tambuwal, Sanata Dino Melaye, Sanata Jumoke Akinjide, Sanata Biodun Olujimi, tsohon Gwamna Ayodele Fayose, Olusegun Mimiko da Olagunsoye Oyinlola.

Sauran manyan baki da suka halarci taron sun hada da: zababben gwamnan Osun, Sanata Ademola Adeleke; ‘Yan takarar Gwamna, Ladi Adebutu (Ogun) da Jide Adediran (Lagos).

Sauran manyan baki sun hada da Eyitayo Jegrde, Babangida Aliyu Muazu, Babban Cif Raymond Dokpesi da Dattijo Wole Oyelese da dai sauransu.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, dukkan wakilan na kan hanyar zuwa dakin taro na Ogunlesi inda mambobin yankin Kudu maso Yamma za su gana da dan takarar shugaban kasa da tawagarsa.

Cikakkun bayanai daga baya…

N.O

Leave A Reply

Your email address will not be published.