Take a fresh look at your lifestyle.

ANC Mai Mulkin Afirka Ta Kudu Ta Goyi Bayan Yunkurin ‘Yan Adawa Na Rufe Ofishin Jakadancin Isra’ila

0 139

ANC mai mulki a Afirka ta Kudu ta ce za ta goyi bayan kudirin majalisar dokokin kasar na rufe ofishin jakadancin Isra’ila da ke Pretoria domin nuna adawa da yakin Gaza.

 

Jam’iyyar ANC ta Afirka ta ce tana kuma goyon bayan kiraye-kirayen da ake yi na gwamnatin kasar ta dakatar da duk wata huldar diflomasiyya da Isra’ila har sai ta amince da tsagaita bude wuta tare da shiga shawarwarin da Majalisar Dinkin Duniya ta samu.

 

Pretoria dai ta dade tana goyon bayan al’ummar Palasdinu, inda jam’iyyar ANC ta kan yi kamanceceniya da nata gwagwarmayar tarihi na yaki da wariyar launin fata.

 

Kakakin jam’iyyar ANC Mahlengi Bhengu-Motsiri ya ce “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar ayyukan kisan kare dangi na gwamnatin Isra’ila.” “Majalisar dokokin Afirka za ta amince da kudirin majalisar dokokin kasar da ke kira ga gwamnati da ta rufe ofishin jakadancin Isra’ila a Afirka ta Kudu.”

 

An gabatar da kudirin majalisar da ake nazari a ranar Alhamis din da ta gabata ne daga jam’iyyar adawa ta Economic Freedom Fighters (EFF) mai ra’ayin rikau.

 

Ba ya dauri kuma zai buƙaci amincewar gwamnati domin aiwatarwa.

 

Yakin da ke tsakanin Isra’ila da Hamas ya samo asali ne sakamakon harin da Palasdinawa suka kai kan kasar Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba daga zirin Gaza, wanda take iko da shi.

 

A wani mataki na ramuwar gayya, Isra’ila ta lashi takobin “kalla” Hamas, ba tare da kakkautawa ba, tana kai hare-hare kan yankunan da aka yi wa kawanya inda kungiyar ta kasance.

 

 

Africanews/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *