Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ne ke jagorantar taron majalisar tattalin arzikin kasa (NEC).
Taron wanda aka fara shi da karfe 10:25 agogon GMT, yana gudana ne a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da ministan kudi, Wale Edun; Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu; da Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali-Pate.
Sauran sun hada da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello; Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa; Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun; Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi; Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara; Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna; Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa; da Gwamna Alex Otti na jihar Abia.
Mataimakan Gwamnonin jihohin Enugu, Gombe, Kano, Zamfara, Katsina, Sokoto, Kebbi, Borno, Osun, Oyo da dai sauran su na halartar taron.
Majalisar ta kan zama bisa doka a kowane wata don duba yadda tattalin arzikin kasar ke gudanar da ayyukanta tare da duba matakan da ya kamata a dauka domin bunkasa tattalin arzikin kasar. Haka kuma tana baiwa shugaban kasa shawara kan yadda zai kyautata rayuwa ga ‘yan kasa.
Leave a Reply