Take a fresh look at your lifestyle.

SDP Ta Kaddamar Da Sabuwar Hedikwata A Abuja

Abdulkarim Rabiu, Abuja

0 58

Shugaban jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Alhaji Shehu Musa Gabam ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gyara matsalolin tsaro da kasar nan ke fuskanta kafin babban zaben 2023.

Shugaban jam’iyyar na kasa ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yayin bikin bude sabuwar hedikwatar jam’iyyar a Abuja.

Ya bayyana cewa, da yanayin tsaro da ake fama da shi a kasar nan, gudanar da zabe mai girman gaske ba zai yiwu ba idan ba a samu zaman lafiya da tsaro kafin zaben ba.

Ya kara da cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ita kadai ba za ta iya bada tabbacin gudanar da zabe cikin lumana da kwanciyar hankali ba, idan shugaban kasar bai dauki matakan da ake bukata ba, don ganin an shawo kan lamarin.

Tun da farko, yayin kaddamar da hedkwatar jam’iyyar na zamani, tsohon dan takarar shugaban kasa Cif Olu Falae ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su bari son rai ya yi tasiri akansu, sannan kada su yadda yansiyasa daga manyan jamyyusu yaudare su.

Hakazalika, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP Prince Adewale Adebayo ya ce abin da SDP ke kawo wa ‘yan Najeriya farin doki ne kawai wanda ke nuna nasara da wadata.

“Saboda talauci ba ya tsoron Allah kuma ba dabi’a ba ne, idan ba a yaki talauci ba, zai haifar da ‘ya’ya marasa tarbiyya, wanda hakan kan Kai ga wanzuwar rashin tsaro ne,” inji shi.

Ak

Leave A Reply

Your email address will not be published.