Take a fresh look at your lifestyle.

Kebbi Guber: Kotun Daukaka Kara Ta Amince Da Zaben Gwamna Idris

0 193

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da zaben Nasir Idris a matsayin zababben gwamnan jihar Kebbi da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

 

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Juma’a, ta yi watsi da karar da jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP da dan takararta na gwamna, Janar Aminu Bande suka shigar a gabanta saboda rashin cancanta.

 

A wani hukunci na bai-daya da mai shari’a Ndukwe Anyannwu ya yanke, kotun daukaka kara ta warware dukkan batutuwa biyar da aka tsara domin tabbatar da goyon bayan gwamnan da kuma PDP.

 

Mai shari’a Anyanwu ya bayyana cewa ba a kafa tuhume-tuhume na jabu na shaidar da aka gabatar wa mataimakin gwamnan jihar, Abubakar Tafida ba kamar yadda doka ta tanada.

 

Ta kuma kara da cewa, batutuwan rashin bin tanadin dokar zabe wajen gudanar da zaben ba za su iya tsayawa ba saboda wadanda suka shigar da kara sun kasa tabbatar da yadda zarge-zargen ya shafi zaben.

 

Daga bisani mai shari’a Anyanwu ya tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kebbi wadda tun farko ta yi watsi da karar da PDP ta shigar tare da tabbatar da zaben gwamna Nasir Idris.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *