Take a fresh look at your lifestyle.

An Kashe Akalla Mutane Tara A Pakistan

0 161

Wata gobara ta tashi a wata cibiyar kasuwanci a birnin Karachi da ke kudancin Pakistan, inda ta kashe akalla mutane tara, kamar yadda jami’ai da kafofin yada labaran kasar suka bayyana.

 

Rahoton ya ce gobarar ta tashi ne da sanyin safiya a wani katafaren kantin sayar da kayayyaki na RJ da ke birni mafi yawan jama’a a Pakistan, kuma jami’an kashe gobara sun ceci mutane kusan 50 amma wasu sun rage a cikin ginin.

 

Magajin garin Karachi, Murtaza Siddiqui ya tabbatar a wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X cewa akalla gawarwakin mutane tara aka mika zuwa asibitocin yankin bayan gobarar.

 

“Ana ci gaba da tsarin bincike ,” in ji shi.

 

Ba a dai bayyana musabbabin tashin gobarar ba.

 

Rahoton ya ce mutane da dama da suka jikkata a gobarar kuma suna jinya a asibiti.

 

 

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *