Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Dr Shamsudeen Usman a matsayin shugaban hukumar gudanarwar ma’aikatar kudi (MOFI).
Shugaban ya kuma amince da nadin Dr Armstrong Ume Takang a matsayin Babban Daraktan MOFI yayin da wasu takwas kuma aka nada su a mukamai daban-daban na hukumar.
Dokta Tajudeen Datti Ahmed shine sabon Babban Darakta na Gudanar da Fayil, Mista Femi Ogunseinde – Babban Darakta, Gudanar da Zuba Jari, Misis Oluwakemi Owonubi – Babban Darakta.
Sauran wadanda aka nada a matsayin Darakta ba na zartarwa ba sun hada da Mista Ike Chioke, Ms Chantelle Abdul, Mista Alheri Nyako, da Mista Bolaji Rafiu Elelu.
Kakakin Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce shugaban na sa ran samun babban sakamako mai inganci daga hukumar gudanarwa ta MOFI.
Hakazalika, shugaban ya kuma nada Dokta Aba Ibrahim da Dr. Muda Yusuf, da su yi aiki a hukumar kwastam ta kasa (NCS) na tsawon shekaru hudu (4) a matsayin wakilan kamfanoni masu zaman kansu.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply