Take a fresh look at your lifestyle.

UMYU Ta Karrama Tsohon Gwamnan Katsina, Ibrahim Shema

Kamilu Lawal,Katsina.

76 417

Tsangayar nazarin aikin sharia ta jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) dake jihar Katsina arewa maso yammacin Najeriya ta karrama tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema.

 

Bikin karrama tsohon gwamnan ya gudana ne a babban dakin taro na jami’ar dake mazaunin jami’ar cikin batagarawa jihar Katsina.

 

Da yake jawabi a wajen bikin karramawar, mataimakin shugaban jami’ar (VC) Farfesa, Shehu Salihu Muhammad ya bayyana cewa karramawar na da nufin nuna godiya ga tsohon gwamnan bisa la’akari da gudummuwar da ya bada wajen cigaban jami’ar da jihar Katsina baki daya.

 

Yace Ibrahim Shema ya bada mahimmiyar gudummuwa wajen bunkasa jami’ar a lokacin da yake gwamnan Katsina.

 

“Mun hadu ne a yanzu domin dukkanin mu mu nuna godiyarmu gare shi bisa ayyukan da yayi mana a lokacin da ya jagoranci wannan jihar wadda wannan jami’a take matsayin mallakinta.

 

“Tarihin wannan jami’an ba zai taba mantawa da mai girma tsohon gwamna, Ibrahim Shema ba, hakan ne ma yasa muke jinjinama wannan tsangaya ta nazarin aikin sharia ta wannan jami’an bisa wannan kyakkyawan tunani na karrama shi da lambar yabo”, inji Farfesa Salihu.

 

Ya kara da cewa ayyukan da tsohon gwamnan ya gudanar a jami’ar abubuwa ne wadanda al’ummar wannan jami’ar da shugabanninta da ma duk wani dalibi da shugabancin wannan jami’an zasu kasance masu alfahari da su a lokaci mai tsawo da zai zo nan gaba.

 

Yace” Mai girma Ibrahim Shema ne ya jajirce wajen kafa wannan tsangaya ta nazarin aikin shari’a tare da tabbatar da samuwar kwararrun malaman tsangayar da gine gine hadi da dukkanin kayan da tsangayar take bukata wanda ya kwato matsayin da take a yau”.

 

Farfesa Shehu Muhammad yayi nuni da cewa daga cikin nuna godiya ga tsohon gwamnan ne ma yasa jami’ar ta sanyama cibiyar da ya gina mata, ta nazari da binciken makamashi dake jami’ar sunan shi “Ibrahim Shema Centre For Renewable Energy And Research” (ISSCeRER) wadda ake sa ran, ba da jimawa ba zata iya gogayya da takwarorinta na jihohin Najeriya ta bangaren bincike da horaswa hadi da zama dalilin samuwar tallafi irin na cikin gida da kasashen ketare

 

Bikin karrama tsohon gwamnan ya samu halartar gwamnan jihar Katsina wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Alhaji Farouk Jobe da shugaban jami’ar  (Chancellor) da shugaban kwamitin gudanarwar jami’ar da Iyalai da yan’uwa hadi da abokai da masu fatan Alheri

 

Gwamnan jihar wanda ya samu wakilin mataimakin sa Farouk Lawal jobe ya bayyana  Ibrahim Shema a matsayin tsayayyen shugaba kuma nagartacce wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen inganta rayuwar al’umma.

 

Yace” Ibrahim Shema ya mulki jihar Katsina a tsawon shekara takwas cikin salo na kwarewa da sanin makamar aiki, ya bayar da gudummuwa sosai wajen habbaka jihar, musamman a bangaren ilmi da rayuwar matasa”.

 

 

Kamilu Lawal.

76 responses to “UMYU Ta Karrama Tsohon Gwamnan Katsina, Ibrahim Shema”

  1. It’s really a nice and helpful piece of info.
    I am happy that you just shared this helpful information with us.
    Please stay us up to date like this. Thanks for sharing.

    my blog post: 토토사이트 (Nestor)

  2. Кто ты есть на самом деле? В чем твое
    предназначение? В каком направлении лежит
    твой путь и как тебе по нему идти?

    Дизайн Человека расскажет об этом!

    – Позволяет жить в согласии со своей природой
    – Снижает тревожность при выборе – Даёт право
    быть собой – Снимает давление социальных стереотипов – Даёт право быть
    собой – Позволяет выстроить эффективную стратегию жизни и
    карьеры – Снимает чувство вины за “неправильность” –
    Даёт опору на природные механизмы – Позволяет жить в согласии со своей природой

    Всего есть четыре типа (манифесторы, генераторы, проекторы, рефлекторы) людей на планете и
    у каждого из них есть стратегия принятия решения.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *