Take a fresh look at your lifestyle.

Al’amura Za Su Daidaita A Najeriya Idan Aka Aiwatar Da Kasafin Kudin 2024: Sen. Sani Musa

Abdulkarim Rabiu, Abuja

0 140

Shugaban kwamitin kudi na majalisar dattawa sanata Sani Musa Mai wakilitar Neja ta Tsakiya ya bayyan cewa al’amura za su daidaita a Najeriya da zarar an aiwatar da kasafin kudin shekara ta 2024.

Sanata Musa ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya gabatar da rahoton kwamitin hadin guiwa na kudu, tsare tsaren kasafin kudi da lamuni na ciki da wajen Najeriya akan Daftarin Tsarin kasafin kudin Shekarun 2024 da 2025 da kuma 2026 na Naira Triliyan Ashrin da shida, wanda shi ne zai zama ginshiki na kasafin kudin shekara ta 2024 da ake sa ran shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai gabatar a wani zama na hadin guiwa tsakanin majalisun dokokin biyu nan da yan kwanaki kadan.
Da yake gabatar da rahoton Sanata Sani Musa ya ce sun yi la’akari a abubuwa da dama musanman hanyoyin samun kudaden shiga na gwamnati kamar Man fetur, da Kwal da ake hakowa daga karkashin kasa da dai sauransu.

Ya ce a da, an kan samu gangar danyan mai miliyan daya da dubu dari biyu ko kasa da haka a ko wace rana, amma tun da wannan gwamnatin ta shigo sai ya karu yanzu ana samun ganga miliyan daya da dubu dari shida zuwa dari bakwai, wanda hakan ke nuni da cewa kudi za su shigo fiye da yadda aka saba samu ada, sannan farashin mai ya kasance a wuri guda zuwa dan wani lokaci.
“Farashin da aka kawo, mun duba mun ga a shekaru uku da suka gabata, ya suke?, sannan muka yi hasashen nawa za a iya samu bisa yadda ake zaton farashin man zai kasance, sannan muka duba muka ga yadda gwamnati ta kawo haka za ta yiyu akan kasafin kudin shekara mai zuwa.” In ji Sanata Sani Musa.

Ya kare da cewa “akan haka aka dora kasafin kudi na badi, an yi hasashen kudade da yawa za su iya shigowa, inda za ka ga ada akan nemi Karin kusan Naira triliyan goma sha daya domin cike gibin kasafin kudi, amma wannan karon ba za a samu gibi ba saboda sabbin hanyoyin samun kudin shiga da aka bullu da su.” 

Bugu da kari majalisar ta yi kira ga jamian tsaro da su kara karfafa tsaro a yankunan da ake hakar danyen mai domin samun Karin kudaden shiga.

Har wa yau rahoton ya duba yiyuwar sake yin nasari kan al’muran masu zuba jari daga kasashen waje wadanda aka janye musu biyan haraji na kusan shekaru uku domin tabbatar da cewa suna biyan kudin haraji ga kasa.

Dangane da kasafin kudin shekara ta 2024 na Naira biliyan 26 kuwa, Sanata Musa ya ce gwamnati ta yi abin da ya kamata to amma idan farashin mai ya karu ko yawan hakar danyan man ya karu kafin lokacin da za a kawo wa majalisa kasafin kudin, za su sake yin nazari domin yin gyara don kasa ta ci gaba.

Daga karshe Sanata Sani Musa ya yi wa yan Najeriya albishir cewa alkaluma na nuni da cewa abubuwa za su gyaru musanman ta hanyar kasafin kudi da kuma yunkurin dalile duk wasu hanyoyi da ake barnatar da dukiyar gwamnati.

Abdulkarim Rabiu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *