Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Wakilai bukaci Yin Garanbawul Ga jiragen Kasa Dake Jigilar Fasinja Daga Kaduna – Abuja

Abdulkarim Rabiu, Abuja

0 158

Majalisar Wakilan Najeriya tabukaci ma’aikatar sufuri ta tarayyar da duba yiyuwar yin garanbawul ga jiragen kasa dake jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna domin kare lafiya da kiyoyin matafiya.

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kananan Hukumomin Makarfi da Kudan daga Jihar Kaduna, Umar Ajilo ne ya bukaci hakan yayin da Ministan Sufuri Sanata Sa’idu Alkali ya bayyana a gaban Kwamitin sufurin kasa na majalisar wakilai karkashin jarorancin shugaban kwamitin Uwargida Blessing Onuh daga Jihar Biniwai.

Hon. Ajilo ya koka kan yadda tarago-tarago na jiragen kasan suka fara lalacewa inda wasunsu gilasan tagojinsu sun fara fashewa kuma a wani zubin jiragen su kan lallace akan hanya a don haka akwai bukatar daukar matakin gaggawa na gyasu duba da yanayin tsaro a kan hanyar, bukatar da minstan ya ce za gaggauta yin gyaran a cikin mako guda,

Har ila yau Hon Ajilo ya yi korafi akan kudin da ake sayan tikitin shiga jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna inda ya ce ana sayar da tikitin babbar kujera a kan Naira 6500 yayin da ake sayan karamar kujera akan Naira 3500, sabo da haka ya kamata gwamnati ta rage domin talaka ya samu sauki musanman a wannan lokaci da ake fama matsin tattalin arziki.

Kazalika Hon. Ajilo ya bukaci ministan sufurin da a sake yin nazari akan tsarin da ake sayar da tikitin ta yanar gizo, ta yadda ko da fasinja ya makara, jirgin ya tafi ya barshi, zai iya amfani da tikitin a wani jirgin da zai zo a gaba.

Da yake maida martini ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Alkali ya ba da tabbacin cewa zai duba yiyuwar hakan, dalili kenan ya sa suke neman Karin fasaha da za su yi irin wadannan abubuwa.

Abdulkarim Rabiu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *