Take a fresh look at your lifestyle.

Kasar Saliyo Ta Ayyana Dokar Ta-Baci A Fadin Kasar Bayan Harin Da Aka Kai A Barikin Kasar

0 840

Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio, ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasar a ranar Lahadi, bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a babban barikin sojoji da kuma mafi girma a babban birnin kasar Afirka ta Yamma, lamarin da ya haifar da fargabar rashin doka da oda, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karin juyin mulki a yankin.

 

 

‘Yan bindigar da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a sansanin sojoji da ke barikin Wilberforce da ke Freetown babban birnin kasar, da sanyin safiya, a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X wanda a da ake kira Twitter Bio ya ce, jami’an tsaro ne suka fatattake su kuma “an samu kwanciyar hankali. ”

 

“Yayin da hadin gwiwar rundunar tsaron mu ke ci gaba da kawar da ragowar ‘yan ta’addan da suka tsere, an kafa dokar hana fita a fadin kasar kuma an karfafa wa ‘yan kasar gwiwa su zauna a gida,” in ji shi.

 

Ma’aikatar yada labarai da ilimi ta kasar ta kuma ce a cikin wata sanarwa da ta fitar gwamnati da jami’an tsaro ne ke da iko kan lamarin.

 

Kawo yanzu dai ba a bayar da cikakken bayani kan ‘yan bindigar da kuma dalilin kai harin ba.

 

Hotunan bidiyo na kan layi, wadanda ake yaduwa, sun nuna yadda sojoji ke sintiri a titunan Freetwon kuma ana jin karar harbe-harbe.

 

Kungiyar tattalin arzikin yankin yammacin Afirka ta ECOWAS – wacce Saliyo mamba ce ta bayyana lamarin a matsayin wani shiri na “samun makamai da kuma kawo cikas ga zaman lafiya da tsarin mulki a kasar. Kungiyar ECOWAS ta sake nanata cewa ba ta jure wa sauya tsarin mulki ba,” in ji kungiyar a cikin wata sanarwa.

 

An sake zaben shugaban kasar Saliyo a wa’adi na biyu a cikin watan Yuni a wata kuri’a mai cike da takaddama inda babbar jam’iyyar adawa ta kasar ta hada baki da jam’iyyar shi wajen yin magudin zabe.

 

Wannan dai shi ne zaben shugaban kasar karo na biyar tun bayan kawo karshen kazamin yakin basasar da aka shafe shekaru 11 ana yi sama da shekaru 20 da suka gabata wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da lalata tattalin arzikin kasar.

 

Bio na ci gaba da fuskantar suka saboda tabarbarewar yanayin tattalin arziki.

 

Kusan kashi 60% na al’ummar Saliyo fiye da miliyan bakwai na fuskantar talauci, tare da rashin aikin yi na matasa na daya daga cikin mafi girma a yammacin Afirka.

 

 

Africanews/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *