Ga dan takarar shugaban kasar Congo Martin Fayulu, zaben da ke tafe wata dama ce a gare shi na samun nasarar da ya yi imanin cewa an yi masa fashi a zaben da ya gabata a shekarar 2018.
Magoya bayan Fayulu da suka kira shi zababben shugaban kasa, sun yi fito-na-fito a wani gangamin yakin neman zabe a Goma ranar Alhamis.
“Muna dogara ga Shugaba Martin Fayulu, saboda shi ne shugaban kasa [wanda zai iya samar da hadin kan kasa da kuma dagewar siyasa,” in ji wani mai goyon bayansa. “Shekaru biyar kenan ana sace masa nasarar da mutane suka ba shi.”
Fayulu ya sha alwashin yin gwagwarmayar tabbatar da sahihin zabe ta hanyar matsin lamba ga bangaren shari’a da hukumar zabe CENI, wadanda ya yi imanin cewa suna nuna son kai ga shugaban kasar mai ci Felix Tshisekedi.
A watan Oktoba, Fayulu, tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa biyar, sun sanya hannu kan wata sanarwa da suka yi kira da a dauki matakan gaggawa don hana zamba kafin ranar 20 ga Disamba.
Africanews/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply