Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Katsina Ya Raba Takardun Daukar Aiki Ga Sabbin Malaman Makaranta 7,325

Kamilu Lawan,Katsina.

254

Gwamnan jihar Katsina malam Dikko Radda ya kaddamar da rabon takardun daukar aiki ga sabbin malaman makaranta sama da dubu bakwai da suka samu nasarar samun guraben aikin yi domin koyarwa a makarantun jihar

 

An kaddamar da raba takardun daukar aikin ne a gidan gwamnatin jihar dake birnin Katsina, fadar gwamnatin jihar

 

Da yake jawabi jim kadan bayan kaddamar da rabon takardun daukar aikin, gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa daukar dubban ma’aikatan domin koyarwa a makarantun jihar na da nufin inganta harkokin koyo da koyarwa a makarantun firamare da sakandiren jihar, kasancewar ilmin farko shine ginshikin ilmi domin cigaban kowace al’umma

 

Ya bayyana yakinin sa da cewa inganta bangaren ilmin farko a fadin jihar zai tallafawa shirin gwamnatin jihar wajen cimma kudurinta na tabbatar da cewa kowane yaro ko yarinya sun samu ingantaccen ilmi a jihar

 

Gwamna Radda wanda ya kara da cewa daukar sabbin malaman na da nufin magance karancin malaman da wasu makarantun jihar ke fuskanta, ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar zata tabbatar da tura sabbin malaman a makarantun da suka kamata domin kawo karshen karancin ma’aikatan koyarwar a fadin jihar

 

Gwamna Dikko Radda ya tabbatar wa sabbin malaman cewa an kammala shirye shiryen da suka wajaba domin su kama aiki a watan janairun shekara 2024 mai zuwa

 

Ya bayyana cewa daga cikin shirye shiryen akwai shirin horaswar sanin makamar aiki da aka shirya masu domin shiga makarantu da azuzuwan daliban cikin shirin da ya kamata

 

Malam Dikko Radda wanda ya taya sabbin malaman makarantar murnar samun aikin na din din din, ya kuma bukace su da su sanya tsoron Allah da kishin kasa hadi da jajircewa wajen gudanar da aikin su, yana mai cewa yin hakan zai tabbatar da aniyarsu ta maida biki ga karamcin da gwamnatin jihar tayi masu ta hanyar basu guraben aikin yi domin su bada gudummuwar su

 

 

Matasan wadanda suka samu guraben aikin koyarwar sun bayyana kudurin su wajen gudanar aikin su yadda ya kamata domin bada gudummuwarsu  wajen inganta bangaren ilmin

 

Mafi yawan wadanda suka samu guraben aikin koyarwar a jihar ta Katsina dai, matasa ne wadanda sukai aikin malanta a kalkashin shirin koyarwar wuccin gadi na S.Power kafin gwamnatin jihar mai ci yanzu bisa jagorancin malam Dikko Umaru Radda ta yanke shawarar maida su ma’aikatan din din din bayan da ya kafa kwamitin da ya tantance su ta hanyar shirya masu jarabawa tare da zaman tantance su kafin tabbatar da cancantar wadanda suka samu nasara

 

Kawo yanzu dai wadanda suka samu aikin koyarwar su 7,325 na cigaba da karbar takardun kama aikin a shelkwatar hukumar kula da malaman makaranta ta jihar wato “Teachers Service Board” da kuma hukumar kula da ilmin bai daya ta jihar wato SUBEB.

 

 

Kamilu Lawan.

Comments are closed.