Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar Kula Da Shige Da Fice Ta Kasa Ta Yaye Sabbin Jami’ai 146

365

A ranar litinin 18 ga watan Disamba ne Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa ta yaye sabbin jami’an ta guda 146 a dandalin fareti na tsohuwar sakatariya dake Minna Fadar Gwamnatin Jihar Neja dake arewa ta tsakiyar kasar.

Da yake jawabi a wajan bikin yaye sabbin jami’an, ACG Nongo Samuel Shima mai kula da shirya ta D, ya bukaci sabbin jami’an da aka yaye da su dauki damar da suka samu a matsayin wata hanyar yiwa kasar su hidima ta kasancewa masu kishi, da da’a da kuma jajircewa wajan rike gaskiya da amana.

ACG Nongo Samuel Shima ya kara da cewa su himmatu wajan ganin sun gudanar da ayyukan su kamar yadda yakamata, inda ya basu tabbacin hukumar na kula da dukkanin hakkokin su da ya kamata.

ACG Shima ya kuma bukaci sauran alumma da su kasance masu kula da duk wasu baki da zasu zo cikin kasar ta hanyar bincike da kuma sannin hakikanin mutanan domin kare kasar daga miyagu.

Ku tantance su domin ku tabbatar da cewar ba bata gari ba ne.” ACG Nongo.

Bikin yaye sabbin jami’an hukumar kula da shige da fice ta kasa da aka yi, ya sami halartan manyan baki daga sauran hukumomin da jami’an tsaro ciki har da Babban Jami’in Hukumar Kashe Gobara ta Kasa ACG Ahamad Karaye mai kula da jihar Neja, da kuma babban sakatare a Ma’aikatar kananana hukumomi na jihar Neja da sauran manyan baki.

 

Comments are closed.