Babban daraktan tashar jirgin ruwan kasar Benin ya ce, kasar Benin ta janye dakatarwar da ta yi na hana shigo da kayayyaki zuwa Nijar ta tashar ruwan Cotonou, sakamakon takunkumin da aka shafe watanni biyar ana yi kan kasar da aka yi juyin mulki.
Kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta kakabawa Nijar takunkumi bayan juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli wanda sojoji suka hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum.
Matakan sun kai ga rufe kan iyakar kasar da Benin, inda aka samu raguwar kudaden shiga bayan da aka dakatar da jigilar kayayyaki zuwa Nijar ta tashoshin jiragen ruwa.
Babban daraktan tashar Bart Jozef Johan Van Eenoo ya ce “An dage matakin da ya shafi dakatar da kayayyakin da ake shigowa da su kasar Nijar a tashar ruwan Cotonou.”
Ya kara da cewa, an dauki matakin “saboda ingantaccen yanayin gudanar da kayayyaki a tashar jiragen ruwa na Cotonou, musamman rage yawan cunkoso,” in ji shi.
Matakin na zuwa ne kusan mako guda bayan da shugaban kasar Benin Patrice Talon ya yi kira da a gaggauta sake kulla dangantaka tsakanin kasarsa da makwabciyarta Nijar.
Kazalika kasashen biyu sun nuna damuwa kan wani katafaren bututun mai da zai baiwa Nijar damar sayar da danyen ta a kasuwannin duniya a karon farko, ta tashar ruwan Seme na kasar Benin.
Africanews/Ladan Nasidi.