Take a fresh look at your lifestyle.

Adadin Wadanda Cutar Ebola Ta Kashe A Uganda Ya Karu – Ma’aikatar Lafiya

0 416

Ma’aikatar lafiya ta kasar Uganda ta ce karin masu cutar Ebola uku sun mutu a kasar Uganda, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa hudu.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan hukumomi sun tabbatar da bullar cutar.

“A cikin awanni 24 da suka gabata, an sami sabbin mutane uku da suka mutu,” in ji ma’aikatar lafiya a cikin wata sanarwa.

Ya zuwa yanzu ma’aikatar lafiya ta Uganda ta tabbatar da kamuwa da cutar Ebola guda 11, ciki har da mutuwar mutane hudu.

Barkewar cutar a halin yanzu da ake dangantawa da cutar Ebola Sudan, da alama ta faro ne a wani karamin kauye a gundumar Mubende a farkon watan Satumba, in ji hukumomi.

Ana binciken wasu mutane bakwai da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar a garin Mubende mai tazarar kilomita 130 yamma da Kampala babban birnin kasar.

Mutum na farko da ya rasa ransa shi ne wani mutum mai shekaru 24 da ya mutu a farkon makon nan.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce nau’in cutar Ebolan Sudan ba shi da saurin yaduwa, kuma ya nuna raguwar mace-mace a bullar cutar a baya fiye da Ebola Zaire, wani nau’in da ya kashe kusan mutane 2,300 a cikin shekarar 2018-2020 da annobar ta bulla a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

labaran africa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *