Tun bayan da kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar suka sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS, matakin ya janyo martani daban-daban.
Ko da yake bai zo da cikakken mamaki ba, musamman bayan juyin mulkin Nijar a watan Yulin da ya gabata.
Firaministan Burkina Faso ya bayar da hujjar yanke hukuncin a birnin Ouagadougou a ranar Alhamis (Feb.01st).
“A ranar 28 ga watan Janairu, Burkina Faso, Mali da Nijar sun dauki matakin tarihi na ficewa daga kungiyar ECOWAS ta tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, yanke shawara ce da aka yi la’akari sosai da ita wacce ta zo bayan cikakken nazari kan cibiyar da kuma illar da ke tattare da janyewar.” ” in ji Apollinaire Joachim Kyélem de Tambela .
Mahukunta sun yi imanin ECOWAS ba ta cimma burin al’ummar Sahel ba kuma suna mai da kawancen AES ya zama dole.
Firaministan kasar Apollinaire Joachim Kyélem de Tambela ya yi Allah wadai da takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakabawa kasarsa Mali da Nijar sannan ya kuma zargi kungiyar da gaza taimakawa kasashe mambobinta.
“Maimakon ECOWAS na jama’a, kungiyar ta zama kayan aikin fasaha wanda a ƙarshe ya kauce daga ingantacciyar muradin mutanen yammacin Afirka.”
“A matsayin hujja, mun lura da yadda ECOWAS ta nuna halin ko in kula a lokacin da aka yi wa jiga-jigan al’ummar mu kisan gilla, ko kuma yayin da ‘yan’uwan mu ke fama da rikicin bil’adama, ko kuma a lokacin da jihohin mu suka fuskanci yawan tashe-tashen hankula,” in ji shi.
Burkina Faso ta ce ta sanar da kungiyar kasashe 15 game da matakin da ta dauka.
Kasashen AES sun yi kira ga al’ummarsu da su tashi tsaye domin nuna goyon bayansu ga matakin nan da kwanaki masu zuwa.
African news/Ladan Nasidi.