Take a fresh look at your lifestyle.

Jami’an Tsaro, Jami’an INEC Sun Isa Da Wuri Domin Zaben Cike Gurbi A Jihar Ondo

84

An dai lura da tsauraran matakan tsaro sun shiga Ikare-Akoko da kewayen garin gabanin zaben cike gurbi na majalisar wakilai ta mazabar Akoko ta arewa maso gabas da Akoko ta arewa maso yamma na jihar Ondo.

 

Rahoto ya nuna cewa tun da karfe 7:00 na safe agogon kasar, tuni aka sanya tsauraran matakan tsaro a babbar hanyar da ta shiga Ikare-Akoko, hedikwatar karamar hukumar Akoko- Gabas.

 

An ga jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, da jami’an tsaron farin kaya da na Civil Defence da NSCDC da kuma hukumar kula da harkokin tsaro ta Najeriya a wurare masu muhimmanci a cikin garin da kuma wuraren zabe, a daidai lokacin da jami’an tsaro ke cikin motocin sintiri suma suna wajen.

 

Rahoton ya ce jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC sun isa da sassafe mafi yawan wuraren zabe a Ikare yayin da aka ga dimbin masu zabe suna duba sunayensu a cikin rajistar masu zabe da aka manna a bango da alluna.

 

Haka kuma, babu wata harkar kasuwanci a garin domin shaguna da kasuwanni sun kasance a kulle, sannan an ga wasu ’yan kasuwa masu tuka babura ne kawai suna bin hanyar kamar karfe 7:30 na safe agogon kasar.

 

Zaben na bankwana shi ne na cike gurbi a majalisar wakilai ta mazabar Akoko ta arewa maso gabas da Akoko ta arewa maso yamma a jihar Ondo, wanda Mista Olubunmi Tunji-Ojo ya bari.

 

Kujerar ta zama babu kowa bayan shugaba Bola Tinubu ya nada Tunji-Ojo a matsayin ministan harkokin cikin gida a watan Agustan 2023.

 

 

 

NAN/Ladan Nasidi.

Comments are closed.