Take a fresh look at your lifestyle.

INEC Za Ta Gudanar Da Karin Zabe A Taraba

137

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta shirya sake gudanar da zabe a jihar Taraba da kuma sabon zabe a jihar Enugu a ranar 14 ga watan Fabrairu.

 

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na kasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu kada kuri’a Sam Olumekun ya fitar ranar Talata a Abuja.

 

Olumekun ya ce hukumar ta dauki matakin ne a taronta na yau Talata inda ta tattauna da sauran batutuwan da suka hada da sakamakon sake zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

 

An gudanar da zaben fid-da-gwani ne a mazabu tara domin cike guraban kujeru da ya biyo bayan faduwar da mambobin da aka zaba a babban zaben shekarar 2023, na majalisun tarayya da na jihohi.

 

Bugu da kari, an kuma sake gudanar da zaben a mazabu 39 kamar yadda kotun daukaka kara ta zaben ta bayar da umarnin.

 

Olumekun ya ce an kammala zaben cikin nasara a dukkanin mazabun da aka zaba, ban da mazabar tarayya ta Jalingo/Yorro/Zing.

 

Ya ce an dage shelanta karshe na zaben ne saboda yawan kuri’u da aka yi a wasu rumfunan zabe, lamarin da ya yi tasiri wajen tazarar kuri’u a tsakanin ‘yan takarar da suka fi yawan kuri’u.

 

Olumekun ya ce a ranar Laraba ne za a fitar da cikakkun bayanan rumfunan zabe.

 

“Game da sake zaben, an samu tarzoma a rumfuna biyu na mazabar tarayya ta Ikono/Ini ta jihar Akwa Ibom da kuma daukacin runfunan zabe a mazabar jihar Enugu ta Kudu ta jihar Enugu da kuma mazabar Kunchi/Tsanyawa ta jihar Kano.

 

“Wannan ya faru ne saboda tashin hankali, ‘yan daba da kuma sace kayan zabe.

 

“A baya dai hukumar ta dakatar da sake gudanar da zaben a wadannan yankunan kamar yadda sashe na 24(3) na dokar zabe na 20 na 22 ya tanada.

 

“Bayan karin rahotanni daga jami’an mu na Jihohin da abin ya shafa, hukumar ta goyi bayan matakin da jami’in mai kula da masu kada kuri’a ya yanke na bayyana sakamako a mazabar tarayya ta Ikono/Ini, saboda yawan wadanda suka yi rajista a rumfunan zabe biyu bai shafi sakamakon zaben ba.

 

“Hukumar ta kuduri aniyar gudanar da wani zabe a Taraba da kuma sabon zabe a jihar Enugu a ranar Laraba 14 ga watan Fabrairu.

 

“Saboda matsalolin tsaro, za a gudanar da zaben a mazabar Kunchi daTsanyawa na jihar nan gaba, bayan tattaunawa da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki,” inji shi.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.