Take a fresh look at your lifestyle.

Najeriya Za Ta Fara Sakin Abincin Metric Ton 42,000

180

Gwamnatin Najeriya ta ce tana kan matakin karshe na sakin metric ton 42,000 na kayyakin abinci iri-iri domin tallafawa masu karamin karfi a fadin kasar.

 

Gwamnatin ta bayyana cewa ta hannun ma’aikatar noma da samar da abinci ta tarayya, a halin yanzu ana jigilar jimillar metric ton 42,000 na hatsi iri-iri a wurare bakwai na tsare-tsare a kasar nan.

 

A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana cewa matakin na daya daga cikin kokarin gwamnatin Tinubu na samar da hanyoyin magance matsalar karancin abinci da ke addabar kasar.

 

Mista Onanuga ya bayyana cewa “ana yin buhunan hatsin ne domin a kai su ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA.”

 

A cewarsa, “bukatar buhunan hatsin ya haifar da tsaiko saboda sabbin odar da gwamnati ta yi na buhunan.”

 

Mai taimaka wa shugaban kasar ya ci gaba da cewa ‘yan Najeriya ba za su bukaci biyan buhunan hatsi ba, domin suna da kyauta.

 

Ya bayyana cewa, metric tonne 42000 za a kara masa ne da metric ton 60,000 na nikakken shinkafa da Gwamnatin Tarayya za ta saya daga Mega Rice Millers.

 

“Tuni, tare da sanarwar fitar da kayan abinci da ke gabatowa daga Tsarin Dabarun, an sami raguwar farashin kayayyaki a manyan kasuwannin hatsi a kasar,” in ji shi.

 

Onanuga ya nanata matsayin ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari inda ya bayyana cewa “Gwamnatin Najeriya tana kuma bunkasa noman abinci ta hanyar bunkasa noman rani a karkashin shirin bunkasa noma na kasa (NAGS-AP).

 

“An kaddamar da Kashi na Farko na Busasshiyar Noma a watan Nuwamba, 2023.

 

“Ya mayar da hankali ne kan noman alkama a fadin jihohi 15 masu noman alkama, wanda ya kai kadada 118,657, ya kuma hada da manoma 107,429.

 

“A yanzu gonakin sun yi kore kuma za a fara girbi nan da makwanni. Akwai rahotanni masu ban sha’awa na karuwar alkama daga jihar Jigawa, wanda a halin yanzu ake shirin girbi daga kimanin hekta 50,000, hekta 10,000 fiye da yadda aka ware tun farko a karkashin shirin.”

 

Lokacin Noman Rani Mataki na 2

 

Ministan Noma, Abubakar Kyari ya ce nan ba da dadewa ba za a fara aikin noman rani na biyu a dukkan jihohin Najeriya 36 da babban birnin tarayya Abuja.

 

Kyari ya kuma bayyana cewa wannan zai shafi shinkafa, masara, da rogo.

 

Yace; “Domin shinkafa, an yi niyya noma hekta 250,000 wanda zai shafi manoma 500,000 tare da sa ran samar da metric ton miliyan 1 na shinkafa .

 

“Ga masara, muna noman hekta 55,000 tare da manoma 110,000 ta haka za mu kara metric ton 165,000 a noman masara na kasa yayin da rogo, muna yin kadada 35,000 tare da manoma 70,000 don samar da tan 525,000 na rogo.

 

“Aikin NAGS-AP yana ba da tallafin kashi 50%. Duk da haka, gwamnatin Najeriya tana ba da ƙarin tallafi ga mataki na 2, wanda zai kawo jimillar tallafin zuwa kusan kashi 93 cikin 100 ga manoman da suke noma amfanin gona.

 

“Haka kuma gwamnoni daban-daban suna nuna goyon baya mai karfi, don kara inganta tallafin.”

 

“Bugu da kari kuma, ana tura famfunan ruwa masu amfani da hasken rana don ban ruwa, wanda gwamnatin Najeriya ta samar, don taimakawa a matakin da ke tafe na shirin.” a cewar Kyari .

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.