Take a fresh look at your lifestyle.

Kasar Guinea Ta Nada Mamadou Bah A Matsayin Sabon Firaminista

200

Gwamnatin mulkin sojan kasar ta nada tsohon madugun ‘yan adawar kasar Guinea Mamadou Oury Bah a matsayin Firaminista, mako guda bayan da ta rusa gwamnatin ba zato ba tsammani.

 

Nadin nasa ya zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna rashin gamsuwa da mulkin soja.

 

An kashe mutane biyu a ranar Litinin bayan da ‘yan sanda suka yi arangama da masu zanga-zanga a wani yajin aikin ma’aikata a fadin kasar.

 

Kungiyoyin kwadago dai na neman rage farashin kayan abinci yayin da ‘yan kasar Guinea ke kokawa da tsadar rayuwa.

 

Mista Bah, wanda aka fi sani da Bah Oury a Guinea, ya bukaci kungiyoyin kwadago da su janye yajin aikin, su kuma bayyana abin da za mu iya yi tare domin magance manyan kalubalen sannu a hankali, mataki-mataki.

 

Ana sa ran kwararren masanin tattalin arziki ba wai kawai zai kafa sabuwar gwamnati da za ta maye gurbin gwamnatin da aka kora ba, har ma da daukar matakan rage wahalhalun tattalin arziki da miliyoyin ‘yan kasar ta Guinea ke fuskanta.

 

Shugaban rikon kwarya Mamady Doumbouya ne ya halarta rantsar da sabon firaminista, wanda ya jagoranci sojojin Guinea wajen hambarar da zababben shugaban kasar Alpha Condé a watan Satumban 2021.

 

Mista Bah, mai shekaru 65, ya kasance sananne a siyasar Guinea tun farkon shekarun 1990. Ya taba zama ministan sulhu a gwamnatin da aka kafa a shekarar 2007.

 

Ya shafe shekaru hudu yana gudun hijira a Faransa bayan da aka damke shi a harin da aka kai gidan shugaba Condé a shekara ta 2011, amma ya koma gida a shekara ta 2016 bayan shugaban ya yi masa afuwa.

 

Ana sa ran kasar Guinea za ta gudanar da zabe domin maido da mulkin dimokuradiyya nan da watanni 10, lokacin da wa’adin mika mulki na watanni 24 da gwamnatin mulkin soja da kungiyar Ecowas ya kayyade.

 

 

 

BBC/Ladan Nasidi.

Comments are closed.