Kungiyar mafarauta a jihar kebbi sunyi nasarar karban shanu 74 a hannun barayi, bayan musayar wuta a kauyen Jarkuka dake karamar hukumar Arewa a jihar kebbi.
Shugaban kungiyar ta madarauta, Musa Hussaini Rambo shine ya bayya na hakan ga manema labarai a ofishin su dake Birnin Kebbi.
Shugaban kungiyar ta Mafarauta, Musa Hussaini Rambo yace kungiyar su, na tallafawa Jami’an tsaro don kawo karshen yan- taada a Kasa baki daya.
Shugaban kungiyar ta Mafarauta Musa Husaini Rambo ya Kara da cewar, sun yi nasarar kama Auwalu Musa da Labaran Umar Wanda suka kware a shiga Transformer da kuma satar wayoyin wutan latarki a cikin garin Birnin Kebbi.
Daya daga cikin barayin Auwalu Musa Wanda ke da Aure har da yara biyu, ya gayawa yan- jaridu cewar tsadar rayuwa ya saka shi shiga wannan Sana’ar na sata.
Tuni dai, kungiyar Mafarautan suka mika masu laifin ga Jami’an tsaro ta civil defence don gudanar da cikakkiyar bincike.
BINTA ALIYU.