Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da rahotannin da kafafen yada labarai ke yadawa na cewa an dakatar ko kuma an janye tattaunawa kan kudirin gyaran haraji.
Da yake jawabi a zaman taron a ranar Alhamis, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sake jaddada aniyar majalisar na aiwatar da kudurin sake fasalin haraji.
Sanata Akpabio ya jaddada cewa babu wani bangare na aikin majalisar da aka dakatar ko janyewa.
Shugaban majalisar dattawan ya ce majalisar na ci gaba da mai da hankali kan aikin ta na wakiltar muradun ‘yan Najeriya kuma ba za ta ji tsoro daga waje ba.
Dangane da batun oda da shugaban majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar, Sanata Akpabio ya yi watsi da rahotannin da kafafen yada labarai ke yadawa da ke nuna cewa an dakatar da tattaunawa kan kudirorin.
Da yake watsi da duk wani yunkuri na matsin lamba a zauren majalisar, shugaban majalisar ya kuma bayyana cewa ba za a iya cin zarafin majalisar ba.
“Ba za a iya cin zarafin Majalisar Dattawa ba. Duk wani garambawul da muka gamsu zai biya bukatun ‘yan Najeriya zamu tabbatar da shi. Wadannan kudirorin sun kunshi tanade-tanade wadanda za su amfanar da jama’a.”
Sanata Akpabio ya jaddada cewa majalisar dattawan ba ta gaggawa kuma za ta yi cikakken aiki a kan kudirorin da ke gaban majalisar saboda haka ya kara daukar matakan kafa doka a kan kudirorin da suka hada da kafa wani kwamiti na musamman mai wakiltar shiyyoyi shida na siyasa a Najeriya da zasu tattaunawa da Lauya. Akanta Janar na Tarayya (AGF), Lateef Fagbemi, domin magance matsalolin da ke haifar da rikici.
Karanta: Fadar Shugaban Kasa Ta Kare Kudirin Gyara Haraji
Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa taron jin ra’ayin jama’a da tuntubar masu ruwa da tsaki da suka hada da gwamnoni da malaman addini da ‘yan kasuwa ya zama wajibi a warware duk wani rashin tabbas.
“Idan makonni shida ba su isa ba, za mu tsawaita lokacin. Mun kuduri anniyar tabbatar da gaskiya da magance duk wata damuwa,” inji shi.
Shugaban Majalisar Dattawan a cikin jawabin nasa, ya kuma yi gargadin a guji yada labaran karya daga kafafen sada zumunta ko kuma rahotannin kafafen yada labarai, inda ya bukaci jama’a su mai da hankali kan gaskiya.
“Ba mu dakatar ko janye tattaunawa kan kudirin gyaran haraji ba. Duk wani yunƙuri na tsoratar da majalisar dattawan bai dace ba. Waɗannan sadarwa ne na zartarwa, kuma sashin zartarwa ne kawai zai iya janye su. Mun ci gaba da tsayawa tsayin daka a kan ayyukan mu na majalisa.”
Sanata Bamidele ya sake jaddada ’yancin kan majalisar, yana mai cewa ‘yan majalisar ba sa karbar umarni daga kowa ko wani ofishi.
“Ba ma karɓar umarni daga kowa ko kowane ofishi, komai girman shi.”
A ranar Laraba a zauren Majalisa, Majalisar Dattawa ta kafa wani kwamiti da zai yi nazari a kan zarge-zargen da ake yi game da batun sake fasalin haraji da ke gaban Majalisar Dokoki ta Kasa.
A cewar mataimakin shugaban majalisar dattawa, Jibrin Barau, wanda ya jagoranci zaman majalisar a ranar Laraba, kwamitin da ke karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Sanata Abba Moro (PDP, Benuwai ta Kudu) zai gana da babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, domin magana kan wuraren da ke cikin kudurorin da kuma komawa Majalisar Dattawa kafin jin ra’ayoyin jama’a.
Sanata Barau ya ce bangaren zartaswa na gwamnati ya amince da majalisar dattawa kan bukatar warware dukkan matsalolin da ke haifar da sabani a cikin kudirorin.
A ranar 3 ga watan Oktoba ne dai shugaban kasa Bola Tinubu ya mika wa majalisar dokokin kasar wasu kudiri hudu na sake fasalin haraji.
Kudurorin sune; daftarin dokar harajin Najeriya na 2024, daftarin kula da haraji, daftarin kafa hukumar tattara kudaden shiga ta Najeriya, da kuma dokar kafa hukumar tattara kudaden shiga ta hadin gwiwa.
Shugaba Tinubu ya ce kudirin za su karfafa hukumomin kasafin kudin Najeriya tare da daidaita manyan manufofin gwamnatin shi.
Ladan Nasidi.