Mataimakin shugaban kasar Ghana kuma dan takarar jam’iyya mai mulki, Mahamudu Bawumia, ya amince da shan kaye a ranar Lahadi ga madugun ‘yan adawa kuma tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama. Zaben shugaban kasa mai cike da takaddama ya nuna gagarumin sauyi na siyasa a kasar da ke yammacin Afirka, inda Mahama ya sake karbar ragamar shugabancin kasar bayan yakin neman zabe.
Gabanin sanarwar a hukumance, Bawumia ya shaidawa manema labarai cewa yana mutunta shawarar da ‘yan Ghana suka yanke na kada kuri’ar neman sauyi. “Na kira mai girma John Mahama don taya shi murna a matsayin zababben shugaban kasar Ghana,” in ji shi.
An gudanar da bukukuwa a sassan kasar ciki har da Accra babban birnin kasar.
An gudanar da zaben ne bisa ga koma bayan matsalar tsadar rayuwa mafi muni a kasar a cikin tsararraki da dama, kuma ana kallonta a matsayin wata babbar jarrabawa ga demokradiyya a yankin da tashe-tashen hankula da juyin mulki suka girgiza.
Bawumia dai ya tsaya takarar ne a matsayin mai rike da tutar jam’iyyar New Patriotic Party, ko NPP mai mulki, wacce ta yi ta fama da matsalar tattalin arziki a karkashin shugaba mai barin gado Nana Akufo-Addo.
Ana kallon nasarar da Mahama ya samu ne biyo bayan sabon salo na zabuka a duniya, inda ke fifita jam’iyyun adawa da masu rike da madafun iko, daga Amurka zuwa kasashen Turai irin su Birtaniya da Faransa da kuma Afirka ta Kudu.
Mahama, mai shekaru 65, ya kasance shugaban kasar Ghana tsakanin Yuli 2012 zuwa Janairu 2017.
Africanews/Ladan Nasidi.